Katsina
Gwamna Dikko Radda ya sake jaddada matsayar gwamnatinsa na ƙin amincewa da yin sulhu da ’yan bindiga, sai dai ya bayyana buɗaɗɗen goyon bayansa ga kowace hanya da za ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da magance matsalolin tsaro a jihar.

Ya bayyana hakan ne a ranar jiya yayin bikin kammala horar da ajin na uku na *Community Watch Corps (CWC)*, inda ya bayyana cewa tattaunawar da ake gudanarwa da ’yan bindiga a wasu sassan jihar ba ta da nasaba da gwamnatin jihar, illa dai ƙoƙarin da al’ummomin yankunan da abin ya shafa ke yi.
Gwamnan ya bayyana wannan hanya a matsayin Katsina Model, wato tsari da al’umma ke jagoranta gaba ɗaya, wanda ke bai wa mazauna yankunan da abin ya shafa damar shiga tattaunawa da ’yan bindigan da suka tuba kuma suka amince da aje makamansu.
Nagarifmradio