INDA RANKA: Wani matashi mai suna Lawal Faruq ya fusata ya banka wa budurwarsa wuta, saboda haushin rabuwar da suka yi duk da alkawarin da suka dauka cewa ba za su taba rabuwa ba.
INDA RANKA: Wani matashi mai suna Lawal Faruq ya fusata ya banka wa budurwarsa wuta, saboda haushin rabuwar da suka yi duk da alkawarin da suka dauka cewa ba za su taba rabuwa ba.
Daga Jaridar Muryoyi
Jaridar Muryoyi ta ruwaito cewa jami’an tsaro sun cafke Lawal Faruq bayan ya banka wa budurwarsa, Omolola Hassan, wuta a kasuwar Mami da ke barikin Odogbo, Ibadan, Jihar Oyo.
Bayanin ya nuna cewa Faruq ya zuba mata fetur sannan ya kunna wuta ya jefa mata sakamakon fushin rabuwar da suka yi. Sojojin da ke barikin sun hanzarta kashe wutar tare da garzaya da ita asibitin Yawiri da ke Akobo domin ceton rayuwarta.
Faruq ya bayyana cewa sun yi rantsuwa da budurwar ba za su rabu ba, amma ta karya alkawarin, abin da ya tayar masa da hankali. Ana ci gaba da bincike, yayin da ake tsare da shi a hannun hukuma.
Nagarifmradio