Rahotanni daga Ćaramar hukumar Birnin-Gwari da ke Jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar mutane akalla bakwai a wani rikici da ya Éarke tsakanin masu haĆar maâadinai ba bisa Ćaâida ba da kuma Ć´an bindiga.
- By NAGARIFMNEWS --
- Saturday, 18 Oct, 2025

- 212 views
Rahotanni daga Ćaramar hukumar Birnin-Gwari da ke Jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar mutane akalla bakwai a wani rikici da ya Éarke tsakanin masu haĆar maâadinai ba bisa Ćaâida ba da kuma Ć´an bindiga.
Wani mazaunin yankin, Umar Maishanu, ya bayyana wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin Ćarfe 11:00 na safe, a ranar Alhamis, a yankin Kuyello da ke gabashin Birnin-Gwari, kusa da iyakar jihohin Zamfara da Katsina.
Maishanu ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan wani Éan bindiga daga jihar Zamfara ya iso wurin haĆar maâadinai domin karÉar haraji daga hannun masu haĆar, amma sai suka kashe shi suka kuma binne gawarsa.
Lamarin ya fusata abokan aikinsa daga cikin Ć´an bindigar, inda suka dawo da tarin jamaâa suka kai farmaki a wurin haĆar maâadinan domin ramuwar gayya, inda suka hallaka mutum bakwai daga cikinsu.
Duk da cewa rundunar Ć´an sanda ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba tukuna, majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa an tura jamiâan tsaro na haÉin gwiwa domin hana Ćarin tarzoma.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa an kama wasu daga cikin Ć´an bindigar da suka fito daga jihar Zamfara, bayan artabu da jamiâan tsaro.
Nagarifmradio




