Rahotanni daga ƙaramar hukumar Birnin-Gwari da ke Jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar mutane akalla bakwai a wani rikici da ya ɓarke tsakanin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma ƴan bindiga.
Rahotanni daga ƙaramar hukumar Birnin-Gwari da ke Jihar Kaduna sun tabbatar da mutuwar mutane akalla bakwai a wani rikici da ya ɓarke tsakanin masu haƙar ma’adinai ba bisa ƙa’ida ba da kuma ƴan bindiga.
Wani mazaunin yankin, Umar Maishanu, ya bayyana wa manema labarai cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe, a ranar Alhamis, a yankin Kuyello da ke gabashin Birnin-Gwari, kusa da iyakar jihohin Zamfara da Katsina.
Maishanu ya bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan wani ɗan bindiga daga jihar Zamfara ya iso wurin haƙar ma’adinai domin karɓar haraji daga hannun masu haƙar, amma sai suka kashe shi suka kuma binne gawarsa.
Lamarin ya fusata abokan aikinsa daga cikin ƴan bindigar, inda suka dawo da tarin jama’a suka kai farmaki a wurin haƙar ma’adinan domin ramuwar gayya, inda suka hallaka mutum bakwai daga cikinsu.
Duk da cewa rundunar ƴan sanda ba ta fitar da sanarwa a hukumance ba tukuna, majiyoyi daga yankin sun tabbatar da cewa an tura jami’an tsaro na haɗin gwiwa domin hana ƙarin tarzoma.
Rahotanni sun kuma bayyana cewa an kama wasu daga cikin ƴan bindigar da suka fito daga jihar Zamfara, bayan artabu da jami’an tsaro.
Nagarifmradio




