An Kama Janar da Wasu Manyan Sojoji Bisa Zargin Shirya Juyin Mulki ga Shugaba Tinubu
An Kama Janar da Wasu Manyan Sojoji Bisa Zargin Shirya Juyin Mulki ga Shugaba Tinubu
Rahotanni daga Sahara Reporters sun bayyana cewa Hukumar Tsaron Ƙasa ta Najeriya (Defence Intelligence Agency – DIA) ta kama Janar na Rundunar Soja tare da wasu manyan jami’an soja 15 bisa zargin shirya juyin mulki domin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wata majiya daga cikin hukumar ta tabbatar da cewa jami’an, waɗanda ke daga matakin Captain zuwa Brigadier-General, sun fara gudanar da tarurruka na sirri da nufin kifar da gwamnati saboda abin da suka kira “cin hanci da rashawa da son kai a cikin siyasar ƙasar”.
A cewar majiyar: “Wadannan jami’an sojoji suna shirin juyin mulki ne don su kifar da gwamnatin Shugaba Tinubu da sauran manyan ‘yan siyasa. Hukumar tsaro ta gano shirin tun kafin su aiwatar da shi, ta kuma kama su a gidajensu daban-daban a fadin ƙasar.”
A baya, rundunar sojin Najeriya ta fitar da wata sanarwa inda ta ce an kama jami’an ne bisa laifin “rashawa da rashin ladabi da karya ƙa’idojin aiki”, tana mai cewa wasu daga cikinsu sun kasa samun karin girma saboda “gazawa a jarabawar karin matsayi”.
Sai dai majiyoyin tsaro sun bayyana cewa wannan sanarwa ba cikakkiya ba ce, domin a zahiri an kama su ne saboda zargin juyin mulki.
Wani babban jami’in tsaro ya ce bikin ranar ‘yancin kai na watan Oktoba 1, 2025 an soke shi saboda tsoron cewa shirin juyin mulkin zai gudana a wannan lokacin.
“Rahotannin sirri sun nuna cewa sun shirya harin juyin mulki ne a lokacin baje kolin Soja na ranar 1 ga Oktoba, inda za su bude wuta kan Shugaban Ƙasa da sauran jami’an gwamnati. Wannan ne ya sa aka soke baje kolin domin kare rayukan manyan shugabannin kasar.”
A halin yanzu, jami’an 16 ɗin na ci gaba da fuskantar tsarewa a hedikwatar Defence Intelligence Agency (DIA) da ke Abuja, yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike a kansu.
Tun bayan samun ‘yancin kai a 1960, Najeriya ta fuskanci juyin mulki guda biyar da suka yi nasara, inda duka suka haifar da sauye-sauyen mulki a cikin tarihi.
Shahara news




