Ƴan bindiga sun sato shanu, sun kora 200 cikin gonaki bayan kakaba harajin miliyan huɗu ga wasu ƙauyuka a Katsina
Ƴan bindiga sun sato shanu, sun kora 200 cikin gonaki bayan kakaba harajin miliyan huɗu ga wasu ƙauyuka a Katsina
Ƴan bindiga sun kakaba harajin naira miliyan huɗu (₦4m) ga mazauna wasu yankuna na jihar Katsina, tare da barazana cewa idan ba su biya ba za su rasa amfanin gonakinsu.
Ƴan bindiga sun sato shanu, sun kora 200 cikin gonaki bayan kakaba harajin miliyan huɗu ga ƙauyuka a Katsina
Rahotanni daga jihar Katsina na nuna cewa wasu ƴan bindiga sun kakaba harajin naira miliyan huɗu (₦4,000,000) ga mazauna wasu ƙauyuka, tare da gargadin cewa idan ba su biya ba, za su rasa amfanin gonakinsu.
Majiyoyi sun ce ƴan ta’addan sun kuma sato shanu da dama, sannan suka kora sama da shanu 200 zuwa cikin daji bayan kai hari a yankin.
Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida cewa maharan sun bayyana musu cewa dole ne su tara kudin harajin kafin su ci gaba da shiga gonakinsu.
Ya ƙara da cewa: “Sun ce idan ba mu biya ba, ba za mu girbe amfanin gona ba. Haka kuma sun kwace shanun wasu manoma.”
Rundunar ‘yan sanda a jihar Katsina dai ba ta fitar da cikakken bayani kan lamarin ba tukuna, sai dai majiyoyi sun tabbatar da cewa jami’an tsaro sun fara bincike don gano inda aka tafi da shanun da kuma dakile irin wannan barazana a yankin.
Nagarifmradio




