Kotun Majistire mai lamba 7 da ke Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Halima Wali, ta bayar da umarni ga Hukumar Hisbah da ta shirya ɗaurin aure tsakanin Idris Mai Wushirya da Basira Yar Guda cikin wa’adin kwanaki 60.

Arewa Updates ta gano cewa kotun ta kuma umarci Shugaban Hukumar Tace Fina-finai ta Kano da ya kasance mai lura da tabbatar da an aiwatar da auren kamar yadda kotu ta tanada.

Mai Shari’a Halima Wali ta bayyana cewa idan aka gaza cika wannan umarni cikin wa’adin da aka tsara, za a sake gurfanar da su a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa laifin rashin bin doka.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)