Dole a Kula da Kafofin Sada Zumunta Domin Labaran Ƙarya na Barazana ga Tsaron Ƙasa nan.

Dole a Kula da Kafofin Sada Zumunta Domin Labaran Ƙarya na Barazana ga Tsaron Ƙasa nan. 

Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar, ya yi kira ga gwamnati da ta dauki mataki wajen sanya doka da oda kan kafafen sada zumunta, sakamakon yaduwar labaran ƙarya da suke haddasa rikice-rikice a ƙasar nan.

Da yake jawabi a Taron  Sarakunan Gargajiya na Arewa da aka gudanar a Birnin Kebbi a yau Talata, Sultan ya bayyana damuwarsa kan yadda labaran ƙarya ke saurin bazuwa cikin sauki a shafukan sada zumunta, kuma mutane da dama na gaskata su ba tare da tantance gaskiya labaran ba.

Ya yi gargadin cewa wannan al’amari na iya haifar da barazana ga zaman lafiya da hadin kan ƙasa.

Sarkin Musulmi ya ce, “Lokaci ya yi da gwamnati za ta kula da harkokin kafofin sada zumunta a ƙasar nan. Yaduwar labaran ƙarya abu ne mai matuƙar haɗari kuma dole ne a dakile shi.”

Har ila yau , ya yaba da ƙoƙarin da dakarun sojin Najeriya ke yi wajen yaki da ‘yan bindiga, yana mai cewa da ba don ayyukan da suke yi ba, da taron ba zai yiwu a jahar Kebbi ba.

“Ina Allah wadai da kalaman cin zarafi da wasu ke yi wa sojojinmu saboda wasu matsalolin da suke fuskanta. Su na bakin kokarinsu wajen dawo da zaman lafiya a sassan ƙasa. Irin waɗannan maganganu ba sa amfani, sai dai su rage musu ƙwarin guiwa,” in ji shi.

A nasa jawabin na maraba, Mataimakin Shugaban Zauren Sarakunan Arewa kuma Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi, ya bayyana cewa taken taron na bana — “Ƙarfafa Haɗin Kan Al’umma Don Samar da Dorewar Zaman Lafiya da Tsaro a Arewa” — ya nuna cikakken goyon baya wajen fuskantar matsalolin tsaro ta hanyar tattaunawa da hadin gwuiwa.

Ya jaddada muhimmancin bai wa sarakunan gargajiya damar taka rawa wajen magance matsalolin tsaro, yana mai cewa sun fi kowa kusanci da al’umma. 

Taron ya samu halartar Gwamnan Jahar Kebbi, Dr. Nasir Idris, Ministan Kasafin Kuɗi, da Etsu Nupe, tare da sauran sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)