Dole a Kula da Kafofin Sada Zumunta Domin Labaran Ćarya na Barazana ga Tsaron Ćasa nan.
- By NAGARIFMNEWS --
- Tuesday, 21 Oct, 2025

- 383 views
Dole a Kula da Kafofin Sada Zumunta Domin Labaran Ćarya na Barazana ga Tsaron Ćasa nan.Â
Sarkin Musulmi, Muhammad Saâad Abubakar, ya yi kira ga gwamnati da ta dauki mataki wajen sanya doka da oda kan kafafen sada zumunta, sakamakon yaduwar labaran Ćarya da suke haddasa rikice-rikice a Ćasar nan.
Da yake jawabi a Taron Sarakunan Gargajiya na Arewa da aka gudanar a Birnin Kebbi a yau Talata, Sultan ya bayyana damuwarsa kan yadda labaran Ćarya ke saurin bazuwa cikin sauki a shafukan sada zumunta, kuma mutane da dama na gaskata su ba tare da tantance gaskiya labaran ba.
Ya yi gargadin cewa wannan alâamari na iya haifar da barazana ga zaman lafiya da hadin kan Ćasa.
Sarkin Musulmi ya ce, âLokaci ya yi da gwamnati za ta kula da harkokin kafofin sada zumunta a Ćasar nan. Yaduwar labaran Ćarya abu ne mai matuĆar haÉari kuma dole ne a dakile shi.â
Har ila yau , ya yaba da ĆoĆarin da dakarun sojin Najeriya ke yi wajen yaki da âyan bindiga, yana mai cewa da ba don ayyukan da suke yi ba, da taron ba zai yiwu a jahar Kebbi ba.
âIna Allah wadai da kalaman cin zarafi da wasu ke yi wa sojojinmu saboda wasu matsalolin da suke fuskanta. Su na bakin kokarinsu wajen dawo da zaman lafiya a sassan Ćasa. Irin waÉannan maganganu ba sa amfani, sai dai su rage musu Ćwarin guiwa,â in ji shi.
A nasa jawabin na maraba, Mataimakin Shugaban Zauren Sarakunan Arewa kuma Shehun Borno, Abubakar Ibn Umar Garbai Elkanemi, ya bayyana cewa taken taron na bana â âĆarfafa HaÉin Kan Alâumma Don Samar da Dorewar Zaman Lafiya da Tsaro a Arewaâ â ya nuna cikakken goyon baya wajen fuskantar matsalolin tsaro ta hanyar tattaunawa da hadin gwuiwa.
Ya jaddada muhimmancin bai wa sarakunan gargajiya damar taka rawa wajen magance matsalolin tsaro, yana mai cewa sun fi kowa kusanci da alâumma.Â
Taron ya samu halartar Gwamnan Jahar Kebbi, Dr. Nasir Idris, Ministan Kasafin KuÉi, da Etsu Nupe, tare da sauran sarakunan gargajiya daga sassa daban-daban na Arewacin Najeriya.
Nagarifmradio




