Hatsarin Tankar Mai a Neja: Mutane 35 Sun Rasa Rayukansu, 46 Sun Jikkata Yayin Da Suke Dibar Mai — FRSC
Hatsarin Tankar Mai a Neja: Mutane 35 Sun Rasa Rayukansu, 46 Sun Jikkata Yayin Da Suke Dibar Mai — FRSC
Hukumar Kiyaye Haddura ta Ƙasa (FRSC) ta tabbatar da cewa mutane 35 sun mutu, yayin da wasu 46 suka jikkata sakamakon fashewar wata tankar mai a kan hanyar Bida–Agaie, kusa da ƙauyen Essa da ke ƙaramar hukumar Katcha, jihar Neja.
Kwamandar FRSC a jihar, Aishatu Sa’adu, ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Minna yau Talata.
Ta bayyana cewa hatsarin ya auku ne bayan da wasu mazauna yankin suka taru suna ƙoƙarin dibar man fetur daga cikin tankar da ta fadi, sai daga bisani ta kama da wuta ta tashi.
“Mun samu damar ceto wasu daga cikin waɗanda suka jikkata tare da taimakon mazauna yankin da wasu masu son taimako, inda muka garzaya da su zuwa Asibitin Tarayya (FMC) da ke Bida,” in ji Sa’adu.
Ta ƙara da cewa binciken farko ya nuna cewa tankar ta fadi ne sakamakon matsalar birki da direban ya fuskanta yayin da yake tafiya.
Kwamandar ta yi kira ga direbobi da su rika bin ƙa’idojin hanya da taka-tsantsan a lokacin tuƙi, tare da gargadin jama’a da su guji dibar mai daga motar da ta yi hatsari, domin hakan babban haɗari ne da ya riga ya janyo asarar rayuka da dama a baya.




