Hatsarin Tankar Mai a Neja: Mutane 35 Sun Rasa Rayukansu, 46 Sun Jikkata Yayin Da Suke Dibar Mai â FRSC
- By NAGARIFMNEWS --
- Tuesday, 21 Oct, 2025

- 193 views
Hatsarin Tankar Mai a Neja: Mutane 35 Sun Rasa Rayukansu, 46 Sun Jikkata Yayin Da Suke Dibar Mai â FRSC
Hukumar Kiyaye Haddura ta Ćasa (FRSC) ta tabbatar da cewa mutane 35 sun mutu, yayin da wasu 46 suka jikkata sakamakon fashewar wata tankar mai a kan hanyar BidaâAgaie, kusa da Ćauyen Essa da ke Ćaramar hukumar Katcha, jihar Neja.
Kwamandar FRSC a jihar, Aishatu Saâadu, ta tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai a Minna yau Talata.
Ta bayyana cewa hatsarin ya auku ne bayan da wasu mazauna yankin suka taru suna ĆoĆarin dibar man fetur daga cikin tankar da ta fadi, sai daga bisani ta kama da wuta ta tashi.
âMun samu damar ceto wasu daga cikin waÉanda suka jikkata tare da taimakon mazauna yankin da wasu masu son taimako, inda muka garzaya da su zuwa Asibitin Tarayya (FMC) da ke Bida,â in ji Saâadu.
Ta Ćara da cewa binciken farko ya nuna cewa tankar ta fadi ne sakamakon matsalar birki da direban ya fuskanta yayin da yake tafiya.
Kwamandar ta yi kira ga direbobi da su rika bin Ćaâidojin hanya da taka-tsantsan a lokacin tuĆi, tare da gargadin jamaâa da su guji dibar mai daga motar da ta yi hatsari, domin hakan babban haÉari ne da ya riga ya janyo asarar rayuka da dama a baya.




