Majalisar Dattawa Ta Nemi A Kara Albashi Ga Sojoji Da Jami’an Tsaro

Majalisar Dattawa Ta Nemi A Kara Albashi Ga Sojoji Da Jami’an Tsaro

Majalisar Dattawan Najeriya ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakin kara albashi da alawus ga sojoji da sauran jami’an tsaro, sakamakon tsadar rayuwa da matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a kasar.

Sanata Ali Ndume, mai wakiltar mazabar Borno ta Kudu, ne ya gabatar da kudurin mai taken “Bukataccen Karin Albashi da Inganta Yanayin Aiki ga Sojoji da Jami’an Tsaro” a yayin zaman majalisar na ranar Talata.

A cewar Ndume, sojojin Najeriya suna fuskantar hadari a kowace rana domin kare martabar kasa, amma albashinsu bai yi daidai da irin sadaukarwar da suke yi ba. Ya bayyana cewa mafi karancin albashi ga matasan sojoji yana tsakanin ₦50,000 zuwa ₦60,000 — adadi da ya kira “kadan idan aka kwatanta da tsadar rayuwa da hauhawar farashi.”

Sanatan ya kuma kwatanta wannan da wasu kasashen Afirka kamar Ghana, Kenya, Masar da Afirka ta Kudu, inda sojoji ke karɓar albashi mai tsakanin ₦180,000 zuwa ₦280,000 a wata, yana mai cewa ya dace Najeriya ta yi koyi da su.

Bayan tattaunawa, majalisar ta umarci Ma’aikatar Tsaro, Ma’aikatar Kudi, da Hukumar Albashi ta Kasa su gudanar da cikakken bita domin daidaita albashin jami’an tsaro da ka’idojin kasa da kasa.

Sanata Ndume ya kara jaddada cewa kara albashi da inganta yanayin aiki ga dakarun tsaro ba wai alfarma ba ce, illa wajibci ne da zai karfafa musu gwiwa da kuma inganta tsaron kasa baki daya.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)