Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta raba naira biliyan 32.9 ga jihohi da cibiyoyin lafiya kafin ƙarshen watan Oktoba domin inganta harkokin kiwon lafiyar jama’a.

Gwamnatin Najeriya ta bayyana cewa za ta raba naira biliyan 32.9 ga jihohi da cibiyoyin lafiya kafin ƙarshen watan Oktoba domin inganta harkokin kiwon lafiyar jama’a.

Saboda haka, gwamnati ta ƙaddamar da sabbin tsare-tsare na wani asusu da aka tanada domin kula da kiwon lafiya a matakin farko (BHCPF), da nufin tabbatar da cewa kuɗin da za a raba za a yi amfani da su yadda ya dace wajen inganta ayyukan lafiya a faɗin ƙasar.

Ministan Lafiya da Walwalar Jama’a, Farfesa Muhammad Pate, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Laraba, yayin ƙaddamar da sabon tsarin BHCPF 2.0, wanda ke mai da hankali kan gaskiya, inganci, da biyan sakamako bisa ga aiki.

A cewarsa, “Wannan mataki yana da alaƙa da umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tabbatar da gaskiya da ingantaccen amfani da kuɗaɗen gwamnati da na abokan hulɗa.”

Gwamnati ta kuma bayyana cewa adadin cibiyoyin lafiya da ke cin gajiyar kuɗin BHCPF zai ƙaru daga 8,800 zuwa 13,000.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)