Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke manyan hafsoshin tsaron ƙasar tare da naɗa sababbi.

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya sauke manyan hafsoshin tsaron ƙasar tare da naɗa sababbi.

Arewa Updates ta ruwaito cewa wannan na cikin wata sanarwa da Mai Ba wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai, Sunday Dare, ya fitar a ranar Jumu’a, 24 ga Oktoba, 2025.

A cewar sanarwar, Janar Olufemi Oluyede ne ya maye gurbin Janar Christopher Musa a matsayin sabon Babban Hafsan Tsaro, yayin da Manjo Janar W. Shaibu ya zama Babban Hafsan Soja.

Haka kuma, Air Vice Marshall S.K. Aneke shi ne sabon Babban Hafsan Sojin Sama, sai Rear Admiral I. Abbas da aka naÉ—a Babban Hafsan Sojin Ruwa.

An tabbatar da cewa Janar E.A.P. Undiendeye zai ci gaba da rike mukaminsa na Babban Daraktan Leken Asiri.

Shugaban Ƙasa ya nuna godiya ga tsoffin hafsoshin da suka kammala wa’adinsu bisa sadaukarwa da kishin ƙasa, tare da kira ga sabbin hafsoshin da su ƙara jajircewa wajen tabbatar da tsaro da haɗin kai a cikin rundunonin soji.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)