WHO tare da haɗin-gwiwa da UNICEF, da gidauniyar chigari da gidauniyar Sultan, Solina, da kuma hukumar bayar da lafiya matakin farko, za suyi wa yara sama da miliyan 1.8, allurar rigakafin Shan-Inna, (polio) a faɗin Jihar Zamfara.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO tare da haɗin-gwiwa da UNICEF, da gidauniyar chigari da gidauniyar Sultan, Solina, da kuma hukumar bayar da lafiya matakin farko, za suyi wa yara sama da miliyan 1.8, allurar rigakafin Shan-Inna, (polio) a faɗin Jihar Zamfara.
 
Manajan lamarin, a cibiyar gaggawa ta ayyukan Polio, a jihar Zamfara, Dakta Murtala Ibrahim Salahuddeen ya bayyana haka a wani taron manema labarai don bikin tunawa da ranar Polio ta duniya a jihar a jiya Asabar.
 
A cewarsa, taken ranar Polio ta duniya ta wannan shekarar shine: ‘'Kawo ƙarshen Polio yanzu, kowane yaro ya cancanci makoma mai ƴanci daga Polio”.
 
Dakta Salahuddeen ya jaddada cewa ana iya yaƙi da cutar Shan-Inna, Polio ta hanyar allurar riga-kafi, ilimi da kuma ayyukan al’umma.
 
A cewarsa, ƙungiyoyin bada tallafi za su cigaba da jajircewa wajen yin aiki kafaɗa-da-kafaɗa da sarakunan gargajiya, malaman addinai da al’umma, don tabbatar da nasarar gangamin yaƙi da cutar Shan-Inna a jihar.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)