Abuja

Yan ta’adda sunce zasu tashi Bama-bamai a majalisar wakilan Najeriya.

Yan ta’adda sunce zasu tashi Bama-bamai a majalisar wakilan Najeriya.

Shugaban kwamitin majalisar mai kula da harkokin tsaron cikin gida Garba Muhammad a yau Talata ya bayyana cewa majalisar dokokin kasar ta samu barazanar ‘yan ta’adda na kai bama-bamai a harabar ginin tare da yin kira da a gaggauta yi wa ginin katangar baya a matsayin wani mataki na kare kai.

Garba ya bayyana hakan ne a Abuja a wajen wani taron jin ra’ayin jama’a kan kudirin kafa hukumar tsaro ta majalisar, wanda ke neman inganta harkokin tsaro, da kare ‘yan majalisa da ma’aikata da masu ziyara a majalisar dokokin kasar. 

Jaridar Punch ta rawaito cewar Ginin da ya kunshi Majalisar Dattawa, Majalisar Wakilai da ofisoshi daban-daban, a cewarsa, yana fuskantar kalubalen tsaro da suka hada da matsalar satar motoci da babura, barna, katin shaida na bogi, da kuma kutsawa daga maziyartan da ba su yi rajista ba.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)