Shugaba Tinubu ya yiwa Maryam Sanda afuwa daga Kisa zuwa daurin shekaru 12 amma ya cire sauran masu laifuka masu tsanani daga jerin wadanda za a yi wa afuwa
Shugaba Tinubu ya yiwa Maryam Sanda afuwa daga Kisa zuwa daurin shekaru 12 amma ya cire sauran masu laifuka masu tsanani daga jerin wadanda za a yi wa afuwa
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan takardun bayar da afuwa ga wasu mutane da aka yanke wa hukunci, bayan ya kammala aiwatar da ikon da kundin tsarin mulki ya ba shi na bayar da afuwa.
Muryoyi ta ruwaito bayan tattaunawa da majalisar koli da kuma samun ra’ayoyin jama’a, shugaban kasa ya sake duba jerin sunayen wadanda za su amfana, inda aka cire masu laifuka masu tsanani kamar garkuwa da mutane, fataucin miyagun kwayoyi, da mallakar makamai ba bisa ka’ida ba.
Tinubu ya ce matakin ya zama dole ne domin kare tsaron kasa da kuma girmama hakkokin wadanda abin ya shafa.
Haka kuma, shugaban kasa ya umarci a mayar da ofishin kwamitin bayar da afuwa daga Ma’aikatar Harkokin Musamman zuwa Ma’aikatar Shari’a, tare da umartar babban lauyan kasa da ya samar da sabbin ka’idoji don tabbatar da gaskiya da bin doka a duk wani shirin bayar da afuwa nan gaba.
Nagarifmradio




