Jahar Sokoto
Ƴan Bindiga Sun Kashe Shugaban Ƙauye da Mutane Biyu a Jihar Sokoto
Ƴan Bindiga Sun Kashe Shugaban Ƙauye da Mutane Biyu a Jihar Sokoto
Rikicin ‘yan bindiga ya sake daukar sabon salo a jihar Sokoto, inda wasu mahara suka kai farmaki a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Tangaza, suka kashe shugaban ƙauye mai rikon ƙwarya tare da wasu mutane biyu.
Wata majiya daga yankin ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun shiga ƙauyen da dare suna harbe-harbe ba tare da kakkautawa ba, inda suka hallaka mutanen kafin su tsere cikin daji.
Rahotanni sun ce shugaban ƙauyen da aka kashe yana daga cikin masu jajircewa wajen kafa ƙungiyar tsaron ƙauye domin kare al’umma daga hare-haren ‘yan bindiga.
Lamarin ya jefa mazauna yankin cikin firgici, inda da dama ke tserewa daga gidajensu saboda tsoron ci gaba da hare-hare.
Jami’an tsaro sun tabbatar da cewa an tura runduna ta musamman zuwa yankin domin tabbatar da doka da oda.
Masana da masu sharhi kan al’amuran tsaro na ganin cewa lokaci ya yi da gwamnati za ta ƙara ƙaimi wajen ɗaukar tsauraran matakan tsaro a arewacin ƙasar, domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
“Idan har shugabannin ƙauye suke fuskantar hare-hare, to wa zai rage?” inji wani dattijo daga Tangaza da ya nemi a ɓoye sunansa.
Nagarifmradio




