Wasu Fusatattun Matasa Sun Farmaki Tawagar Gwamnan Neja

Wasu Fusatattun Matasa Sun Farmaki Tawagar Gwamnan Neja

Wasu matasa a garin Bida, Jihar Neja, sun kai hari kan tawagar Gwamnan jihar, Umar Bago, inda suka lalata motocin gwamnati da dama tare da jikkata wasu jami’an gwamnati, kamar yadda jaridar Starnews ta ruwaito.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne sakamakon fusata da matasan suka yi kan alkawarin da gwamnan ya yi musu na raba kuɗi ga al’umma a wani shiri da ake yi gabanin gudanar da zaɓukan ƙananan hukumomi a jihar.

Sai dai a cewar wasu daga cikin matasan, an ci amanarsu, domin a cewarsu, “’yan tsiraru ne kawai daga cikinmu suka samu kuɗin da aka raba,” abin da ya tayar musu da ƙura har ta kai ga tashin hankali.

Shaidu sun ce jami’an tsaro sun yi ƙoƙarin shawo kan lamarin, amma rigimar ta riga ta ɓarke kafin a samu daidaito. An kuma ce gwamnatin jihar ta tabbatar da faruwar lamarin tare da nuna takaici, tana mai cewa za a gudanar da bincike domin gano waɗanda suka haddasa tashin hankalin.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)