Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Kebbi ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane, tare da ceto wani yaro mai shekara 14
Rundunar ‘Yan Sandan Jahar Kebbi ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da yin garkuwa da mutane, tare da ceto wani yaro mai shekara 14 ba, a yayin wani hadin gwiwar samame da jami’an tsaro suka gudanar a ƙauyen Ka’oje, ƙaramar hukumar Bagudo ta jihar.
A cewar sanarwar rundunar, jami’an tsaro sun gudanar da wannan samame ne bayan samun sahihan bayanan sirri kan inda masu garkuwa da mutane suka ɓuya bayan sun sace yaron. An yi nasarar cafke su bayan musayar wuta, inda jami’an suka kubutar da yaron cikin koshin lafiya.
Rundunar ta kuma tabbatar da cewa bincike ya fara domin gano sauran abokan aikinsu da kuma irin hanyoyin da suke bi wajen gudanar da laifin.
Kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya yaba da yadda jami’an tsaro suka nuna ƙwarewa da jajircewa wajen ceto yaron, tare da tabbatar da cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan sintiri da kai farmaki domin kawar da masu aikata laifuka a yankin.
An kama masu garkuwa da mutane biyu a Ka’oje, Bagudo LGA. An kubutar da yaro ɗan shekara 14 cikin la iya. Bincike yana ci gaba don kamo sauran ɓarayin. Rundunar ‘yan sanda ta yi alkawarin ci ga a da tsaurara tsaro a jihar Kebbi.
Nagarifmradio




