Nijer
Ba Za Mu Zuba Ido Amurka Ta Far Wa Najeriya Ba – In Ji Janar Tchiani
Ba Za Mu Zuba Ido Amurka Ta Far Wa Najeriya Ba – In Ji Janar Tchiani
Shugaban ƙasar Nijar, Janar Muhammad Tchiani, ya bayyana cewa ba za su lamunci Amurka ta kai wa Najeriya hari ba, domin su a matsayin ‘yan uwa kasashen arewacin Afirka za su tsaya tsayin daka wajen kare juna.
Janar Tchiani ya ce “Ku bar ta ta yi ƙoƙarin harba harsashi, babu wani makamin da zai iya ratsa sararin samaniyar Nijar ba tare da mun fatattake shi ba. A shirye muke mu afka wa yaƙi gaba da gaba da Amurka matuƙar ta yi gigin kai hari kan ‘yan’uwanmu Najeriya.
Ya kara da cewa lokaci ya yi da kasashen Afrika ke kare juna, ba a bar kasashen waje suna juya su yadda suke so ba.
Nagarifmradio




