Rikicin cikin gida ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan Boko Haram da ISWAP sama da 200
- By NAGARIFMNEWS --
- Monday, 10 Nov, 2025

- 109 views
Rikicin cikin gida ya yi sanadiyyar mutuwar mayakan Boko Haram da ISWAP sama da 200
Rahotanni daga yankin Arewa maso Gabas sun tabbatar da cewa rikici mai tsanani ya barke tsakanin kungiyoyin ta’addanci Boko Haram da ISWAP, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mayaƙa fiye da mutane 200 daga ɓangarorin biyu.
Majiyoyi daga yankin dajin Sambisa da kuma kusa da tafkin Chadi sun bayyana cewa rikicin ya samo asali ne bayan samun sabani kan raba ganima da ikon yankuna a tsakanin shugabannin kungiyoyin.
Wani mazaunin yankin da bai so a bayyana sunansa ba ya shaida wa manema labarai cewa an yi artabu mai ƙarfi da ya ɗauki awanni da dama, inda manyan kwamandoji daga ɓangarorin biyu suka mutu, tare da lalata sansanonin da ke dajin Yuwe da Kafa.
Rahotanni sun ƙara da cewa mayakan ISWAP ne suka fara kai wa Boko Haram farmaki, inda suka ƙone motocin yaki, suka ƙwace makamai, tare da kama wasu daga cikin mayaƙan da suka tsira daga faɗan.
Wata majiya daga rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da cewa an lura da motsin mayaƙan da ke cikin rikici, kuma sojoji suna ci gaba da kai hare-hare a yankunan da lamarin ke gudana domin kammala murkushe ragowar ’yan ta’adda.
A halin yanzu, yankin Yuwe na dajin Sambisa wanda ke tsakanin Borno da iyakar tafkin Chadi ya koma tamkar filin daga, yayin da ake ci gaba da tattara gawarwaki da kuma raunanan mayaƙa.
Nagarifmradio




