Jahar Neja

Muna Biyan ‘Yan Bindiga Naira Miliyan 7 Domin Mu Zauna Lafiya - In Ji Shugaban Al’umma a Neja Wasu mazauna yankin

Muna Biyan ‘Yan Bindiga Naira Miliyan 7 Domin Mu Zauna Lafiya - In Ji Shugaban Al’umma a Neja

Wasu mazauna yankin Shiroro a jihar Neja sun bayyana cewa suna biyan kudin fansa har Naira miliyan bakwai (₦7,000,000) ga ‘yan bindiga a duk wani lokaci domin su sami damar zama cikin gidajensu da kuma gudanar da harkokin noma ba tare da tsangwama ba.

Shugaban al’ummar yankin, Alhaji Yahaya, ne ya bayyana hakan a cikin hirar da aka yi da shi a shirin Tsalle Daya na tashar Prestige FM Minna.

A cewar Alhaji Yahaya, ‘yan ta’addan sun karɓe ikon wasu garuruwa da suka haɗa da Makera, Galapai, Chukuba, Ushaka, Manini, Kawuri, Bakarie I, Utako da Magana, inda kowane mutum mai aure ke bayar da gudunmawar kudi domin a tara adadin da za a miƙa wa ‘yan bindigar.

“Yanzu haka jami’an tsaro sun daina zuwa yin sintiri a yankinmu. Mu kan tara kuɗi mu ba wa ‘yan bindiga don su bar mu mu zauna lafiya,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, ‘yan bindigar kan shigo cikin gari da makamai suna tilasta wa jama’a su biya kuɗin kafin su fice daga yankin.

Al’ummar Shiroro sun bayyana gajiyarsu da wannan matsala, tare da kiran gwamnati — ta jiha da ta tarayya - da ta ɗauki matakan gaggawa domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)