Magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Zamfara sun yi zargin cewa Gwamna Dauda Lawal Dare ya yi almubazzaranci da kusan naira tiriliyan ɗaya da gwamnatin ta karɓa cikin shekaru biyu da suka wuce.
- By NAGARIFMNEWS --
- Tuesday, 18 Nov, 2025

- 101 views
Magoya bayan jam’iyyar PDP a jihar Zamfara sun yi zargin cewa Gwamna Dauda Lawal Dare ya yi almubazzaranci da kusan naira tiriliyan ɗaya da gwamnatin ta karɓa cikin shekaru biyu da suka wuce.
A cewar magoya bayan, lamarin ya jefa su cikin tarin damuwa ganin yadda mulkin ya kasa samar da canjin da ake fata duk da yawan kuɗin da aka samu. Sun bayyana cewa ko da yake an karɓi kuɗaɗe masu yawa, babu wani gagarumin aiki da ke tabbatar da ci-gaba ko ingantuwar rayuwar talakawa, alhali jama’a na ci gaba da fama da tsananin rashin tsaro, talauci da kuma koma bayan al’umma.
Da yake karin haske, sakataren ƙungiyar, Zahraddeen Ibrahim Gusau, ya bayyana abin a matsayin matuƙar abin kunya da rashin karfin gwamnati. Ya ce, “Gwamnati da ta samu kusan tiriliyan ɗaya cikin shekaru biyu bai kamata ta kasa aiwatar da manyan ayyukan ci-gaba ba. Abin takaici, aikin da ake iya gani kawai shi ne gajeren aikin hanyoyi a Gusau, sauran yankuna kuwa babu komai.”
Tun hawowar Gwamna Dauda Lawal Dare, al’amuran yau da kullum a Zamfara sun ci gaba da kasancewa yadda suke. A kusan dukkan kananan hukumomi babu sabbin ayyuka, babu ingantattun shirye-shirye, kuma babu tsarin magance matsalolin jama’a. Asibitoci suna cikin halin koma-baya, makarantun gwamnati na cikin mawuyacin hali, kuma babu kayan aiki na zamani da za su sauƙaƙa rayuwar al’umma.
Zahraddeen ya kara da cewa jama’ar Zamfara sun fara kallon gwamnatin a matsayin wadda ta fifita ’yan ƙalilan da ke kusa da gwamnati. Ya ce, “Abin mamaki ne a ga gwamnati da jama’a suka zaba ta koma mallakar wasu mutane biyu, Barau da Mato—mutanen da ba ma ’yan asalin Zamfara ba—sun mamaye dukkan al’amuran arzikin jiha, alhali mutanenmu ba su amfana da komai.”
Mutanen jiha da dama sun nuna takaicin cewa ko da yake gwamnatin na samun kuɗaɗe fiye da yadda aka saba, babu wani ci-gaba da ake gani a zahiri. Maimakon haka, ana ganin wasu mutane daga waje ne ke cin gajiyar arzikin jiha, yayin da bukatun jama’a ke fuskantar raina hankali.
Saboda haka, magoya bayan PDP na Zamfara sun bukaci a gudanar da cikakken bincike daga kungiyoyin farar hula, masu zaman kansu da hukumomin sa ido kan yadda gwamnatin Dauda Lawal Dare ta kashe kudaden jihar. Sun ce dole ne a fito da gaskiya domin jama’a su san yadda aka tafiyar da kudaden da suka haura tiriliyan ɗaya.
A ƙarshe, Zahraddeen Ibrahim Gusau ya jaddada cewa, “Zamfara na bukatar shugabanci nagari mai gaskiya da rikon amana. Ba za mu yarda a ci gaba da tafiya a cikin duhu ba yayin da wasu ke amfani da damar mulki don amfanarsu ta kashin kai.”
Nagarifmradio




