Dalibar Kebbi Ɗaya Ta Kuɓuta Daga Hannun Mahara, 24 Har Yanzu Ba a Gano Su Ba Yayin da Sojoji Ke Ƙara Ƙaimi a Ceton Su

Dalibar Kebbi Ɗaya Ta Kuɓuta Daga Hannun Mahara, 24 Har Yanzu Ba a Gano Su Ba Yayin da Sojoji Ke Ƙara Ƙaimi a Ceton Su

Ɗaya daga cikin dalibai mata 25 da aka sace daga Makarantar Sakandaren ‘Yan Mata ta Government Girls Comprehensive Secondary School, Maga, a Jihar Kebbi, ta kuɓuta daga hannun waɗanda suka yi garkuwa da su, yayin da jami’an tsaro ke ƙara kaimi wajen ceto sauran dalibai 24 da suka rage.

Lamarin ya faru ne a daren Litinin lokacin da wasu ’yan bindiga suka kutsa makarantar, suka saci dalibai daga ɗakunan kwanan su, tare da kashe mataimakin shugaban makarantar.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, shugaban makarantar, Musa Rabi Magaji, ya shaida wa kafafen yaɗa labarai na ƙasashen waje cewa dalibar da ta kuɓuta ta yi taɓaɓɓare cikin dazuzzukan da ke kewaye har ta dawo gida da yammacin Litinin, sa’o’i bayan sace su. Ya ƙara da cewa wata daliba ta tsira tun lokacin da maharan suka kai farmakin farko.

“Ina sanar da ku cewa ɗaya daga cikin yaran ita ce cikin waɗanda aka sace 25, ɗayar kuma ta dawo tun da wuri. Dukkansu suna cikin koshin lafiya,” in ji shi.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)