Jirgin mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima, ya sauka a birnin Kebbi domin jajanta wa Gwamnatin jihar bisa sace ’yan matan makarantar Maga.
- By NAGARIFMNEWS --
- Wednesday, 19 Nov, 2025

- 125 views
Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima, ya isa Jihar Kebbi domin ganawa da gwamnatin jihar da iyalan ‘yan mata da aka sace daga Makarantar Sakandare ta ‘Yan Mata ta Gwamnati, Maga, da wasu ‘yan bindiga.
Jirgin saman da ya dauki Shettima ya sauka a Filin Jirgin Sama na Sir Ahmadu Bello da ke Birnin Kebbi tare da Daraktar Janar na Hukumar Kula da Yanayi na Gaggawa ta Kasa (NEMA), Zubaida Umar, da sauran jami’an gwamnati.
Mataimakin Shugaban Kasa ya tashi daga Abuja zuwa Kebbi ne bisa umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Ana sa ran zai isar da sakon Tinubu ga mutanen jihar, tare da karbar rahoto kan lamarin domin sanarwa Shugaban Kasa.
Harin da aka kai makarantar Kebbi ya yi sanadiyyar mutuwar Mataimakin Shugaban Makarantar, Malam Hassan Makuku, wanda rahotanni suka nuna an kashe shi ne yayin da yake kokarin hana ‘yan bindiga sace ‘yan matan.
Nagarifmradio




