mawakiyar Rap ta Amurka Nicki Minaj tace tabbas ana kashe kiristoci a Najeriya.
- By NAGARIFMNEWS --
- Wednesday, 19 Nov, 2025

- 74 views
Shahararriyar mawakiyar Rap ta Amurka, Nicki Minaj, ta bi sahun tsohon shugaban Amurka Donald Trump, inda ta goyi bayan zargin da ya yi cewa ana gudanar da cin zarafi da kisa kan Kiristoci a Najeriya, duk da musun da fadar gwamnatin Abuja ke ci gaba da yi.
A yayin wata tattaunawa da aka gudanar jiya Talata a birnin New York, karkashin jagorancin jakadan Amurka a MDD, Mike Waltz, fitacciyar mawakiyar mai shekaru 42 ta yi godiya ga Shugaba Trump bisa yadda ya dauki wannan batu da muhimmanci.
Nagarifmradio




