Mai Shari’a James Omotosho ya yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai, bayan masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhumar da ke kansa.

Mai Shari’a James Omotosho ya yanke wa Nnamdi Kanu hukuncin ɗaurin rai da rai, bayan masu gabatar da ƙara sun tabbatar da tuhumar da ke kansa.

Tuhume-tuhumen da aka yi wa Kanu sun haɗa da aikata ta’addanci, da kuma tunzura jama’a su kai hari su kashe jami’an ƙananan hukumomi da ‘yan sanda.

A cewar bayanan kotu, masu gabatar da ƙara sun gabatar da shaidu da suka haɗa da bidiyo, rubuce-rubuce, da bayanan sahihan masu gani da ido, waɗanda suka nuna cewa kalaman Kanu da umarninsa sun taka muhimmiyar rawa wajen tayar da tarzoma a wasu yankuna na Kudu maso Gabas.

Kotun ta kuma bayyana cewa wannan hukunci ya biyo bayan dogon zaman sauraron ƙara, da kuma ƙoƙarin da lauyoyin bangarorin biyu suka yi na kare matsayinsu, kafin a cimma matsayar cewa Kanu ya aikata laifukan da ake zarginsa da su.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)