Sai da muka gargadi Makarantar St. Mary’s su rufe makarantar saboda bayanan sirri da aka samu amma suka ki

Sai da muka gargadi Makarantar St. Mary’s su rufe makarantar saboda bayanan sirri da aka samu amma suka ki – inji Gwamnatin Niger

Daga Jaridar Muryoyi

Gwamnatin Jihar Neja ta dora alhakin sace daliban Makarantar St. Mary’s da ke Agwara kan rashin bin umarnin rufe makarantu da ta bayar tun kafin harin ’yan bindiga.

Sakataren Gwamnati, Abubakar Usman, ya bayyana cewa gwamnati ta samu sahihan bayanan leken asiri da suka nuna yiwuwar barazana a yankin Neja ta Arewa, wanda ya sa aka ba da umarni ga dukkan makarantu masu kwana da su rufe na É—an lokaci.

Sai dai duk da wannan gargadi, makarantar St. Mary’s ta koma aiki ba tare da sanar da gwamnati ko neman izini ba, abin da ya jefa dalibai da malamai cikin mawuyacin hali.

Gwamnatin ta tabbatar cewa jami’an tsaro sun fara aikin ceto da bincike, tare da kira ga al’umma da su rika ba da duk wata muhimmiyar bayanai da za su taimaka. Haka kuma an ce za a ɗauki matakin doka kan masu gudanar da makarantar saboda kin bin umarnin da aka bayar.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)