CAN

Fiye da ɗalibai da malamai 200 aka sace a harin da aka kai makarantar Katolika ta Jihar Neja” inji kungiyar – CAN

Fiye da ɗalibai da malamai 200 aka sace a harin da aka kai makarantar Katolika ta Jihar Neja” inji kungiyar – CAN

“Daga cikin bayananmu da muka tattara, mun gano an yi garkuwa da ɗalibai 215 ciki har da malamai 12,” in ji CAN.

Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a Jihar Neja, Bulus Yohanna, ya ce an sace fiye da ɗalibai da malamai 200 lokacin da ‘yan bindiga suka kai hari a wata makarantar Katolika da ke jihar.

Mista Yohanna, wanda ya ce ya ziyarci makarantar, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a.

“Daga bayananmu, ‘yan ta’adda sun yi garkuwa da ɗalibai da kananan yara 215 ciki har da malamai 12,” in ji Yohanna a sanarwar da Reuters ta ruwaito.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)