Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya ce a halin yanzu babu abin da ke damunsa kamar matsalolin tsaron a Arewa.

Shugaban ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya ce a halin yanzu babu abin da ke damunsa kamar matsalolin tsaron a Arewa.

Ya bayyana haka ne yayin taron cikar shekaru 25 da kafuwar Kungiyar Tuntuba ta Arewa (ACF), inda aka kuma kaddamar da wani asusu na tallafawa ayyukan ƙungiyar.

Shugaba Tinubu, ta bakin wakilinsa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, ya ce matsalar tsaro a Arewacin Najeriya na daga cikin manyan abubuwan da ke damunsa, musamman ganin yadda ake ta samun rahotannin sace É—alibai a makarantun yankin kwanakin nan.

Ya kara da cewa gwamnatinsa ta gada matsalolin tsaro a matakai daban-daban, sai dai suna gudanar da ƙoƙari mai ƙarfi don kawo ƙarshen matsalolin cikin gaggawa.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)