Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya tabbatar da cewa an ceto mutane 38 da 'yan bindiga suka yi garkuwa da su a Jihar Kwara.
- By NAGARIFMNEWS --
- Sunday, 23 Nov, 2025

- 88 views
Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa an yi nasarar ceto mutane 38 masu ibada waɗanda ’yan bindiga suka yi garkuwa da su a cocin Eruku da ke Jihar Kwara.
A cewar shugaba Tinubu, jami’an tsaro tare da haÉ—in gwiwar al’umma sun gudanar da aiki ba dare ba rana domin gano inda aka boye mutanen, lamarin da ya kai ga kubutar da su ba tare da wata asara ta rayuka ba.Â
Ya kuma jaddada cewa gwamnatin tarayya ba za ta yi wasa da batun tsaron ’yan kasa ba, tare da tabbatar da ci gaba da ɗaukar matakai domin ganin an kawo ƙarshen hare-haren ’yan bindiga a fadin ƙasar.
Nagarifmradio




