Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Kano, Sun Sace Mutane 25
- By NAGARIFMNEWS --
- Monday, 01 Dec, 2025

- 55 views
Yan Bindiga Sun Sake Kai Hari a Kano, Sun Sace Mutane 25
Daren jiya ya kasance mai firgici a wasu yankuna na jihar Kano, bayan da ’yan bindiga suka kai hari a Unguwar Tsamiya da ke Faruruwa, tare da Dabawa, dukansu a ƙaramar hukumar Shanono.
A cewar mazauna yankin, mutum biyu sun jikkata, sannan aka yi garkuwa da akalla mutane 25.
Abin damuwa shi ne, wannan harin ya faru ne ƙasa da sa’o’i 24 bayan wani makamancin harin da aka kai a Ƴan Kamaye, Tsanyawa, wani yanki da ke iyaka da jihar Katsina.
A halin yanzu, al’ummar yankunan suna cikin yanayin tsoro da rashin tabbas, inda suke kira ga hukumomi da su kawo ɗauki cikin gaggawa.
Wannan rahoton ya fito ne daga Bakatsine, mai sharhi kan harkokin tsaro, wanda ya wallafa a shafinsa na X.
Nagarifmradio




