Jam’iyyar adawa ta ADC a Najeriya ta bukaci tsohon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, da ya ƙi karɓar muƙamin jakada da Shugaban Ƙasa ya naɗa shi.
- By NAGARIFMNEWS --
- Monday, 01 Dec, 2025

- 61 views
Jam’iyyar adawa ta ADC a Najeriya ta bukaci tsohon shugaban hukumar zaɓe ta ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu, da ya ƙi karɓar muƙamin jakada da Shugaban Ƙasa ya naɗa shi.
African Democratic Congress ta bayyana naɗin Farfesa Yakubu — wanda ya bar kujerar shugabancin INEC a watan Oktoban da ya gabata — a matsayin “abin kunya”.
A cewar ADC cikin wata sanarwa, “Nadin Yakubu abin kunya ne kuma rashin sanin ya kamata, musamman ganin yadda ya jagoranci zaɓen da ya haifar da cece-kuce, wanda kuma ya bai wa Shugaban Ƙasa Tinubu nasara, sannan kuma ‘yan makonni bayan barinsa aiki ake son naɗa shi jakada.”
A ranar Asabar ne fadar Shugaban Ƙasa ta bayyana cewa Tinubu ya nemi amincewar majalisar dattawa domin tura jerin jakadu 32 zuwa kasashen waje, ciki har da Farfesa Yakubu.
“Saboda haka, muna kira ga Farfesa Yakubu da ya ƙi karɓar wannan muƙami saboda kishin ƙasa, kare martabar hukumar zaɓe, tabbatar da sahihancin zaɓe mai zuwa, da kuma mutuncinsa,” in ji jam’iyyar.
Nagarifmradio




