Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta sake jaddada matakan hana jigilar fasinja da babura, tare da takunkumin hana amfani da Keke Napep daga karfe 10:00 na dare har zuwa 6:00 na safe a kowace rana.
- By NAGARIFMNEWS --
- Monday, 01 Dec, 2025

- 62 views
Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta sake jaddada matakan hana jigilar fasinja da babura, tare da takunkumin hana amfani da Keke Napep daga karfe 10:00 na dare har zuwa 6:00 na safe a kowace rana.
Â
Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da tsaurara dokokin zirga-zirga, musamman ga masu jigilar fasinja da babura, tare da kakaba takunkumi kan harkar Keke Napep a jihar.
Â
A cikin sanarwar da rundunar ta fitar, an jaddada cewa dokar hana babura ɗaukar fasinja har yanzu tana nan a ƙarfi a wasu muhimman yankuna na Kano, sakamakon ƙarin matsalolin tsaro da ake fuskanta.
Â
Haka kuma, an bayyana cewa daga yanzu Keke Napep ba za su yi aiki daga ƙarfe 10:00 na dare zuwa 6:00 na safe ba, a dukkan ranakun mako. Rundunar ta ce matakin ya zama dole domin dakile laifuka da ake yawan aikatawa da waɗannan hanyoyin sufuri, musamman a lokutan dare.
Â
’Yan sanda sun gargadi masu karya dokar cewa za su fuskanci kamawa, kwace abin hawa da kuma gurfanawa a kotu. Hukumomin tsaro sun ce za su ƙara yawan sintiri da sa ido a wuraren da dokar ta shafa.
Â
Wannan mataki, a cewar rundunar, na daga cikin kokarin gwamnati da jami’an tsaro na farfaɗo da zaman lafiya da rage laifuka a cikin birnin Kano da kewaye.
Â
Â
Nagarifmradio




