Sabon ministan tsaron Najeriya

SHUGABA TINUBU YA NADA JANAR CHRISTOPHER MUSA A MATSAYIN SABON MINISTAN TSARO

SHUGABA TINUBU YA NADA JANAR CHRISTOPHER MUSA A MATSAYIN SABON MINISTAN TSARO

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya nada Janar Christopher Gwabin Musa a matsayin sabon Ministan Tsaro.

A cikin wata wasiƙa da ya aikawa Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, Shugaba Tinubu ya mika sunan Janar Musa domin maye gurbin Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, wanda ya yi murabus a ranar Litinin.

Janar Musa, mai shekara 58 a ranar 25 ga Disamba, babban soja ne da ya yi fice, wanda ya yi aiki a matsayin Shugaban Ma’aikatan Tsaro na Najeriya (CDS) daga shekarar 2023 zuwa Oktoba 2025. Ya lashe Colin Powell Award for Soldiering a 2012.

An haifi Janar Musa a Sokoto a 1967, inda ya yi makarantar firamare da sakandare kafin ya shiga College of Advanced Studies da ke Zariya. Ya kammala a 1986 sannan ya shiga Nigerian Defence Academy (NDA) a wannan shekarar, inda ya samu digirin Bachelor of Science a 1991.

An yi masa komishan a Rundunar Sojojin Najeriya a matsayin Second Lieutenant a 1991, kuma ya yi fice a aikinsa tsawon shekaru. Cikin manyan mukamansa akwai:

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)