Sojojin ƙasar nan a ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun kubutar da mata bakwai tare da yara biyar da aka sace a kan hanyar Gwoza zuwa Limankara.
- By NAGARIFMNEWS --
- Tuesday, 02 Dec, 2025

- 87 views
Sojojin ƙasar nan a ƙarƙashin Operation Hadin Kai sun kubutar da mata bakwai tare da yara biyar da aka sace a kan hanyar Gwoza zuwa Limankara.
wannan bayanin ya fito ne daga wata sanarwa da hedikwatar tsaro ta ƙasar ta fitar a ranar talata.
Sanarwar ta nuna cewa sojoji tare da mafarauta da ’yan sa-kai sun gudanar da wani samame a yankin Uvaha, wanda ya sa ’yan ta’addar suka tsere suka bar mutanen da suka yi garkuwa da su.
Haka kuma sanarwar ta ce sojojin suna ci gaba da gudanar da bincike domin cafke ’yan ta’addar da suka gudu.
An kuma bayyana cewa an mika waÉ—anda aka ceto ga wakilin shugaban karamar hukumar Gwoza domin a haÉ—a su da iyalansu, bayan an tabbatar da samun kulawa ta farko.
Nagarifmradio