An ayyana dokar hana fita ba dare ba rana a Lamurde, Jihar Adamawa, saboda tashin hankalin kabilanci da ya sake kunno kai.

An ayyana dokar hana fita ba dare ba rana a Lamurde, Jihar Adamawa, saboda tashin hankalin kabilanci da ya sake kunno kai.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Adamawa ta bayyana cewa ta fara aiwatar da dokar zaman gida na awa 24 da gwamnatin jihar ta sanar a Lamurde, bayan sake barkewar rikicin kabilanci a wasu yankunan karamar hukumar.

Arewa Updates ta ruwaito cewa wannan bayanin na cikin wata sanarwa da Jami’in Hulɗa da Jama’a na rundunar, SP Suleiman Yahaya Nguroje, ya fitar a ranar Litinin, 8 ga Disamba 2025.

Sanarwar ta bayyana cewa Kwamishinan ’Yan Sanda na jihar, Dankombo Morris, ya aika da ƙarin jami’ai tare da kayayyakin aiki domin tabbatar da bin umarnin dokar zaman gida da kuma dakile duk wani abu da ka iya kara tayar da rikici a yankin.

Har ila yau, sanarwar ta ce rundunar tare da sauran hukumomin tsaro na ci gaba da aiki tare wajen tabbatar da tsaro, tana kuma gargadin jama’a da su nisanci duk wani yunkuri da zai haifar da tarzoma ko tayar da hankalin jama’a.


Comment As:

Comment (0)