Shugaba Tinubu Ya Sake Tabbatar da Janye ’Yan Sanda Daga Tsaron Ministoci da Manyan Mutane, A Bar Su a Hannun Civil Defence
- By NAGARIFMNEWS --
- Wednesday, 10 Dec, 2025

- 26 views
Shugaba Tinubu Ya Sake Tabbatar da Janye ’Yan Sanda Daga Tsaron Ministoci da Manyan Mutane, A Bar Su a Hannun Civil Defence
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada umarninsa na a janye jami’an ’yan sanda nan take daga matsayin masu rakiya ga Manyan Mutane (VIPs) a fadin Najeriya, yana mai jaddada muhimmancin sake tura ma’aikata zuwa gaban ayyukan tsaro a daidai lokacin da kasar ke fuskantar manyan kalubale.
A yayin taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) na ranar Laraba, Shugaban ya ƙara nanata umarnin da tun farko aka bayar a watan Nuwamba, sakamakon rahotannin rashin bin wannan doka a wasu wurare.
Matakin na da nufin magance karancin ma’aikata a Rundunar ’Yan Sandan Najeriya, tare da karfafa aikin ’yan sanda na al’umma, ta hanyar dawo da dubban jami’an da aka ware wa VIP masu zaman kansu domin mayar da su ga yaki da ta’addanci, fashi, da sauran barazanar tsaro.
Nagarifmradio




