Gamayyar Kungiyoyin Mata A Arewa Sun bukaci Dan Bindiga Bello Turji Da Ya Miqa Wuya.
- By NAGARIFMNEWS --
- Friday, 12 Dec, 2025

- 80 views
Gamayyar Kungiyoyin Mata A Arewa Sun bukaci Dan Bindiga Bello Turji Da Ya Miqa Wuya.
Dandalin gamayyar Kungiyoyin Matan na Arewacin najeriya yayi Kira ga Dan bindigar nan Bello Turji Da ya aje makamai ya Miqa Wuya domin Samun Zaman Lapiya.
Kakakin Dandalin gamayyar Kungiyoyin salamatu Bello itace ta bayyana haka a madadin sauran Manbobin Dandalin Jim kadan Bayan kammala Taron da suka Gudanar a ranar juma'a a Birnin tarayya Abuja.
Salamatu tace angudanar da Taron ne da zummar yin adduo'i na musamman GA yankin Arewacin najeriya da kuma Dakaru kazalika da kasa Baki Daya.
Hakama tace dandalin ya Yabama Kokarin Da Dakarun Sojin najeriya sukayi na halaka Dan Bindiga kallamu buzu Wanda jagoran Rundunar Bello Turji ne da suke aika aika a Karamar Hukumar Mulkin sabon Birnin a Jahar Sokoto.
Bayanai sun nuna cewa Dakarun operation hadarin daji sunyi nasarar halaka buzu da Sauran abokan aikinshi Akalla su 8.
Sakamakon wannan nasarar ta halaka buzu, Dan Bindiga Bello Turji ya nuna damuwa matuka tareda yin barazana daukar fansa.
Nagarifmradio




