Jirgin Flybird Ya Yi Hatsari a Kano, Mutane 11 Sun Tsira

Jirgin Flybird Ya Yi Hatsari a Kano, Mutane 11 Sun Tsira

Rahotanni sun tabbatar da cewa mutane 11 sun tsallake rijiya da baya bayan wani jirgin sama mallakin kamfanin Flybird ya yi hatsari a filin jirgin sama na Malam Aminu Kano, da ke birnin Kano.

Lamarin ya faru ne da safiyar Lahadi, lokacin da jirgin — wanda ya taso daga birnin tarayya Abuja — ya isa Kano don sauka, sai dai ya samu matsala yayin ƙoƙarin sauka a titin jirgi (runway).

Shaidu sun ce an samu ɗan girgiza a jikin jirgin yayin saukar, wanda hakan ya haifar da hatsari, sai dai babu wanda ya rasa ransa ko rauni mai tsanani. Jami’an kula da filin jirgin sun ɗauki matakin gaggawa don tabbatar da cewa fasinjojin sun fita lafiya daga jirgin.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Najeriya (NCAA) da hukumar binciken hatsarorin jiragen sama (AIB) sun fara gudanar da bincike domin gano musabbabin hatsarin.

Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake ƙara kiran buƙatar inganta lafiyar jirage da hanyoyin sauka a filayen jiragen sama a Najeriya.


Comment As:

Comment (0)