Harin 'Yan Bindiga Yayi Silar Mutuwar Wani Mutum,Bayan da Wanda Suka kaiwa Harin Yasha Dakyar a Neja.

Harin 'Yan Bindiga Yayi Silar Mutuwar Wani Mutum,Bayan da Wanda Suka kaiwa Harin Yasha Dakyar a Neja.

A Daren Jiya ne da misalin karfe 9:30 zuwa 10:00 na dare wasu da ake Zargin 'Yan bindiga ne,Suka kai sumame garin Shadadi,gundumar Bangi Dake Karamar Hukumar Mariga a Jihar Neja, inda suka shiga cikin gidan wani Magidan ci Tare da Yunkurin wucewa dashi.

Rahotanni sun bayyana cewa Maharan Sun shigo Garin ne Musamman Domin Tafiya da wannan bawan Allah Sedai Basu Samu Damar Tafiya dashi ba.

A Yayin Harin Sunyi nasarar Harbin Mutum Daya da Yayi Sanadiyyar rasa rayuwan sa a cikin garin Shadadi, kamar yadda Mazauna Yankin Suka tabbatar muna.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)