NBA Ta Bukaci Sake Duba Dokokin Haraji a Najeriya

NBA Ta Bukaci Sake Duba Dokokin Haraji a Najeriya

Kungiyar Lauyoyi ta Najeriya (NBA) ta bayyana bukatar gaggawa ga Gwamnatin Tarayya da ta sake duba tare da inganta dokokin haraji na ƙasa, domin su dace da halin tattalin arzikin da ake ciki a yanzu.

A cewar kungiyar, dokokin harajin da ake shirin aiwatarwa daga shekarar 2026 ya kamata su kasance masu adalci, sauƙin fahimta, tare da kare muradun ‘yan ƙasa da ‘yan kasuwa.

NBA ta jaddada cewa sabunta dokokin zai taimaka rage matsin lamba ga talakawa, inganta harkokin kasuwanci da zuba jari, da kuma ƙara yawan kuɗaɗen shiga na gwamnati ba tare da cutar da tattalin arzikin ƙasa ba.

Kungiyar ta kuma bukaci gwamnati ta gudanar da cikakken shawarwari da masu ruwa da tsaki kafin aiwatar da sabbin dokokin, domin kauce wa rikice-rikice da ƙorafe-ƙorafe daga al’umma.

NBA ta ƙara da cewa wajibi ne a tabbatar da cewa duk wani sabon tsarin haraji zai kasance a bayyane, mai gaskiya, tare da bin ƙa’idojin doka da oda.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)