Badakalar KuÉ—aÉ—e: EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 16 kan tsohon ministan shari'a Malami
- By NAGARIFMNEWS --
- Wednesday, 24 Dec, 2025

- 55 views
Badakalar KuÉ—aÉ—e: EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 16 kan tsohon ministan shari'a Malami
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar da tuhume-tuhume 16 na badakalar kuɗaɗe a gaban kotu a kan tsohon ministan shari'a, Abubakar Malami da ɗansa Abdulaziz Malami, da wata ma’aikaciya a kamfanin Rahamaniyya Properties Limited, Hajiya Bashir Asabe.
EFCC ta zargi Malami da safarar kusan Naira biliyan 9 domin sayen gidaje masu tsada a Abuja, Kebbi, Kano da wasu wurare.
 Hukumar ta ce Malami ya mallaki gidaje kusan 30 da kimarsu ta kai Naira biliyan 212.8, mafi yawansu kuma an saya ne a lokacin da yake rike da mukamin Antoni janar na ƙasa daga 2015 zuwa 2023.
A cewar EFCC, an yi amfani da wasu kamfanoni, ciki har da Metropolitan Auto Tech Limited da Meethaq Hotels Limited, wajen ɓoye asalin kuɗaɗen da ake zargin sun samo asali ne daga ayyukan haram, inda aka yi amfani da su wajen sayen kadarori da dama a biranen Abuja, Birnin Kebbi da Kano.
Hukumar ta bayyana cewa tana iya amfani da tanadin kwace kadarori ba tare da hukunci ba (Non-Conviction Asset Forfeiture) don karɓar wasu daga cikin kadarorin, tare da bai wa masu ruwa da tsaki wa’adin kwanaki 14 su nuna dalilin da ya sa kada a kwace su.
Nagarifmradio




