EFCC Na Ci Gaba da Tsare Malami Duk da Umarnin Kotu Kan Bada Beli

EFCC Na Ci Gaba da Tsare Malami Duk da Umarnin Kotu Kan Bada Beli

Hukumar Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Ƙasa (EFCC) na ci gaba da tsare tsohon Ministan Shari’a kuma Antoni Janar na Ƙasa, Abubakar Chika Malami (SAN), duk da umarnin da wata babbar kotu ta bayar na bada belinsa.

Rahotanni sun nuna cewa kotun ta bayar da belin ne bisa wasu sharudda da aka gindaya, sai dai har zuwa yanzu EFCC ba ta sako Malami ba. Wannan lamari ya janyo ce-ce-ku-ce daga masana harkokin shari’a da lauyoyi, inda wasu ke nuna damuwa kan yiwuwar ci gaba da tsare Malami bisa wasu sabbin tuhuma ko bincike daban da hukumar ke gudanarwa a kansa.

Wasu masana doka na bayyana cewa a tsarin shari’a, EFCC na da ikon ci gaba da tsare wanda ake zargi muddin akwai sabon umarnin kotu ko sabbin tuhume-tuhume da ba su da alaƙa da belin da aka bayar. Sai dai sun jaddada muhimmancin mutunta ikon kotu da bin tanadin dokar kasa.

A nata bangaren, wasu magoya bayan Malami da ƙungiyoyin farar hula sun fara nuna damuwa, suna mai kira ga EFCC da ta gaggauta aiwatar da umarnin kotu. Sun ce bayar da beli ba yana nufin an wanke mutum daga tuhuma ba ne, illa dai dama ce ta kare kansa daga waje cikin shari’a mai adalci.

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)