Mutum Uku Sun Rasa Rayukansu a Arangama Tsakanin Jami’an Tsaro da Ƙauraye a Katsina
- By NAGARIFMNEWS --
- Sunday, 28 Dec, 2025

- 23 views
Mutum Uku Sun Rasa Rayukansu a Arangama Tsakanin Jami’an Tsaro da Ƙauraye a Katsina
Akalla mutane uku ne suka rasa rayukansu sakamakon wata arangama da ta ɓarke tsakanin jami’an tsaro da wasu ƙauraye a wata unguwa da ke cikin birnin Katsina, a daren Asabar, 27 ga Disamban 2025.
Rahotanni sun bayyana cewa rikicin ya samo asali ne lokacin da jami’an tsaro suka yi yunƙurin kama wani matashi tare da ƙwace wayarsa. Sai dai yayin da matashin ya yi ƙoƙarin karɓar wayarsa daga hannunsu, lamarin ya rikide zuwa hatsaniya, inda daga bisani aka harbe shi.
Wannan lamari ya haifar da fusata da tashin hankali a tsakanin matasa a yankin, wanda ya janyo rikicin ya ƙara ɗaukar zafi, har ya kai ga rasa rayukan mutane uku. Haka kuma, an kona ofishin jami’an tsaro tare da wasu babura a yankin.
A halin yanzu, rahotanni na nuna cewa ana zaman ɗar-ɗar a unguwar, yayin da mazauna ke cikin fargabar sake ɓarkewar rikici, yayin da hukumomi ke ci gaba da ƙoƙarin shawo kan lamarin.
Nagarifmradio




