A cewar hukumar ta NECO daga watan Nuwamba/Disamba 2025 dukkan jarabawar SSCE za a yi ta da kwamfuta

A cewar hukumar ta NECO daga watan Nuwamba/Disamba 2025 dukkan jarabawar SSCE za a yi ta da kwamfuta, tare da gayyatar masu cibiyoyin CBT masu zaman kansu da suke sha’awar shiga tsarin da su yi rijista bisa ƙa’idoji da tsare-tsare na fasaha da tsaro da kuma kayan aiki da aka tsara. 

Shin kuna ganin wannan sauyi zai taimaka wajen inganta tsarin jarabawa ne ko kuma zai kawo ƙalubale ga ɗalibai?

Ya kuke kallon matsayin dalibai da ba su da kwarewa wajen amfani da naura mai kwakwalwa da wadanda ke zaune a yankunan da ba su da isassun cibiyoyin horarwa?

Me kuke ganin gwamnati da iyaye za su yi don tallafawa É—alibai wajen shirya wa wannan sabon tsari?

Shin cibiyoyin horarwa da ke Najeriya sun isa don ɗaukar ɗaliban duk fadin ƙasar nan?

Shin kuna ganin wannan sabon tsarin zai rage zamba da satar jarrabawa?

Nagarifmradio

Comment As:

Comment (0)