Barca da Real da za su kara a wasan ƙarshe na Copa del Rey

A ranar Asabar ne manyan ƙungiyoyin ƙwallon ƙafa na Sifaniya, Real Madrid da Barcelona za su ɓarje gumi a wasan ƙarshe na gasar Copa del Rey.

Wasan wanda ake yi wa laƙabi da el-classico - na ɗaya daga cikin wasannin da suka fi jan hankalin masoya ƙwallon ƙafa a faɗin duniya.

Ƙungiyoyin sun kawo wannan matakin ne bayan da Real ta doke Real Sociedad da ci 5-4 a wasa gida da waje.

Ita ma Barcelona ta kawo matakin ne bayan fitar da Atletico Madrid da ci 5-4 gida da waje.

Barcelona ce ƙungiyar da ta fi ɗaukar kofin na Copa del Rey a tarihi, bayan da ta ɗauki kofin har sau 31, yayin Real Madrid ta ɗauki kofin sau 20.

A yanzu haka Barcelona ce ta ɗaya a kan teburin La Liga da maki 76, yayin Real Madrid ke matsayi na biyu da maki 72, inda ya rage wasa biyar a ƙarƙare gasar ta bana.

Wasu fitattun ƴan wasan ƙungiyoyin na fama da jinya ciki har da Robert Lewandowski da Eduardo Camavinga, don haka ba za su buga fafatawar ba.

Tuni dai ƙungiyoyin suka fitar da jerin sunayen zaratan ƴan wasan da za su je da su wasan na ƙarshe da za a buga a birnin Seville da ke ƙasar ta Sifaniya.


Comment As:

Comment (0)