Jirgin Saman ValueJet dake Ɗauke da 'Yan Kwallon Super Eagles na Najeriya Yayi Saukar Gaggawa a Angola Saboda Fashewar Gilashi
Jirgin Saman ValueJet dake Ɗauke da 'Yan Kwallon Super Eagles na Najeriya Yayi Saukar Gaggawa a Angola Saboda Fashewar Gilashi
An samu tashin hankali na dan lokaci a yau bayan wani jirgin sama mallakin kamfanin ValueJet da ke dauke da tawagar 'yan kwallon Super Eagles na Najeriya daga kasar Afirka ta Kudu zuwa Najeriya, ya yi saukar gaggawa a Angola saboda an gano fashewar gilashin taga a cikin jirgin.
Wani babban jami’i na Hukumar Kwallon Kafa ta Najeriya (NFF) da ke cikin tawagar ya tabbatar da lamarin ga Sahara Reporters, inda ya bayyana cewa “wani lamari ne mai hadari wanda Allah ya kare.”
Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya tashi daga Afirka ta Kudu ne zuwa Uyo, Jihar Akwa Ibom, inda ake sa ran Super Eagles za su fafata da abokan karawarsu a wasa na karshe na neman gurbin gasar cin kofin duniya ta FIFA 2026.
Sai dai a tsakiyar hanya, matukin jirgin ya gano matsalar gilashin da ya fashe, kuma nan take ya yi saukar gaggawa a kasar Angola domin kauce wa hatsari.
Rariya




