Ćasar Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makaman da kuÉinsu ya kai Dala miliyan 346, kwatankwacin Naira biliyan 530 don yaĆi da taâaddanci.
- By NAGARIFMNEWS --
- Thursday, 14 Aug, 2025

- 123 views
Ćasar Amurka ta amince ta sayar wa Najeriya makaman da kuÉinsu ya kai Dala miliyan 346, kwatankwacin Naira biliyan 530 don yaĆi da taâaddanci.
Makaman da za a siyar sun haÉa da bama-bamai da naâurorin kakkabo jiragen sama da jirage marasa matuka da sauran su.
A cewar Kamfanin Sarrafa Makamai na Amurka (DSCA), za a sayar wa Najeriya makaman ne domin tallafa wa shirinta na yaki da âyan taâadda da masu safarar miyagun Ćwayoyi.
Kamfanin ya sanar da cinikin ne a cikin wata sanarwa ranar Laraba.
A cewar sanarwar, Najeriya ta buĆaci sayen bama-bamai guda 1,002, naâurar kakkabo jirage guda 1,002, sai manyan bindigu guda guda 5,000 da sauran makamai.
Kazalika, Amurkar ta amince ta sayar wa Najeriya helikwaftocin kai hari guda 12 da sauran muggan makaman da darajarsu ta kai Dala miliyan 997 a 2022.
Kamfanin ya ce kamfanonin da aka amince wa su yi kwangilar dillancin makaman su ne Lockheed Martin da RTX.N da kuma BAE.
âWannan cinikin zai taimaka wa bunĆasa hulÉar kasa da kasa da kuma manufofin Amurka a kan harkar tsaro da inganta alaĆa da Najeriya a matsayin babbar Ćawa a yanki Afirka yamma da hamadar Sahara,â in ji sanarwar.




